Kiwon Lafiya
Mun yiwa yara miliyan 100 rigakafin Polio a Afrika – WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, a kalla yara miliyan 100 a yankin Afrika, sun karɓi rigakafin cutar Polio a shekarar da ta gabata.
Shugaban hukumar a yankin Afrika Dr Matshidiso Moeti ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, annobar corona ta ƙara ba da dama wajen gudanar da rigakafin cutar Polio, wanda ake hasashen hakan zai iya kawo ƙarshen cutar a yankin Afrika.
Har yanzu ana ci gaba da binciken asalin corona – WHO
A cewar sa, akwai buƙatar ba da haɗin kai ga WHO don isa yankunan da ba a yiwa yaran su rigakafin ba, duk da cewa afrika ta kai matakin fita daga ƙasashe masu fama da cutar, bayan da ta kwase shekara huɗu ba a samu rahoton masu ɗauke da cutar ba.
You must be logged in to post a comment Login