Labarai
NAPTIP ta ceto yara mata 11 da akayi yunkurin safararsu zuwa Libya
Hukumar yaƙi da fataucin bil-Adama ta Najeriya NAPTIP ta ce, ta ceto wasu yan mata 11 da aka yi yunkurin safararsu daga kasarta zuwa kasar Libya.
A cewar NAPTIP an gudanar da bincike kan yunkurin safarar ‘yan matan daga Jamhuriyar Nijar lokacin da wata ƙungiyar masu safarar mutane ke niyyar jigilar su zuwa ƙasar Libya.
Kwamandan hukumar NAPTIP shiyyar Sokoto, Abubakar Tabrane ya shaida hakan ga manema labarai, yana mai cewa jami’an hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ne suka karɓi ‘yan matan.
Sai dai ya ce, tuni suka fara bincike da nufin kamo waɗanda ake zargi da safarar ƴan matan, wadanda tuni suna hannun hukumar NAPTIP ta Sokoto.
Rahoton:Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login