Labarai
Ni zan jagoranci yaki da Boko Haram- Janar Tukur Burutai
Babban hafsan soji na kasa Janar Tukur Yusuf Buratai, zai koma yankin Arewa maso gabashin kasar nan, don cigaba da jagoranta da gudanar da aikin Sojin kasar nan da kuma yaki da ‘yan Boko Haram.
Janar Burutai, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga Sojin kasar nan na musamman na Special Super Camp, dake garin Ngamdu a karamar hukumar Kaga dake jihar Borno, inda ya shaida musu cewar’ daga yanzu zan kasance tare daku a dukkan kowanne filin daga’.
A wata takarda, da kakakin sojin kasar nan Kanal Sagir Musa, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai, ta sanar da cewa a baya babban hafsan Sojin , ya shiga cikin tawagar da ta kai ziyara ga tawagar sojin da take a gurare daban –daban da suke a gabashin kasar nan wanda ke aikin samar da tsaro a yankin.
Labarai masu alaka.
Rundunar sojan saman kasar nan ta dakile harin Boko Haram
Sojojin Najeriya na fafatawa da yan kungiyar boko haram a jihar Borno
Sanarwar ta kara dacewa, Burutai, ya kai ziyara a sansanin Soji na daya, dake Mulai, da sansani na sha biyu na sojoji na musamman dake Chabbol kusa da birnin Maiduguri, in da ya tattauna dasu tare da yi musu jawabi.
Sanarwar, ta tabbatarwa da al’ummar kasar nan cewa rundunar sojin kasar nan a shirye take data kare rayuka da dukiyoyin jama’a da iyakokin kasar nan a koda yaushe, tare da alwashin kawo karshen ta’addancin ‘yan kungiyar ISWAP,dana Boko Haram, nan ba da dadewa wa ba yankin Arewa maso gabashin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login