Labarai
NLC ta baiwa gwamnati wa’adin makonni biyu ta janye karin farashi
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu na ta janye ƙarin farashin wutar lantarki da na man fetur da ta yi.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar suka gabatar, wadda ta fitar a yammacin jiya laraba, mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa Kwamared Ayuba Wabba.
Jim kaɗan bayan sanarwar, wakilinmu Nasir Salisu Zango ya zanta da shugaban ƙungiyar na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir wanda ya ce, daukar wannan mataki ya zama tilas.
A farkon watan Satumban da muke ciki ne dai gwamnatin tarayya ta yi ƙarin farashin wutar lantarki da kuma na man fetur wanda ya janyo cece-kuce a ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login