Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan kisan manoma
Rundunar sojin Najeriya ta nanata cewa manoma 43 aka kashe, ba 110 da Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe ba.
Mai Magana da yawun rundunar, John Enenche a wata hira da ya yi da gidan talibijin na Channels, ya ce har yanzu suna tattara bayanai kan mutanen da harin ya shafa domin tabbatar da adadin wadanda suka mutu.
Sai dai rundunar ta ce abinda yake kara ta’azzara batun matsalar tsaro shine, yadda mazauna yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula ba sa kai rahoto ga sojoji da sauran hukumomin tsaro kan halin da suke ciki.
“Mutane da dama basa kawo mana rahoton abinda ke addabar su kan sha’anin tsaro, kuma ba dole bane ka tilastawa mutane su sanar maka abinda ke faruwa.” In ji shi
Ko da yake John Enenche ya ki bayyana yanda rundunar sojin ke tattara bayanata akan wuraren da fama da yake-yake a arewacin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login