Labarai
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama ‘yan ta’adda 352
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a Najeriya ta ce ta kama mutane 352 da ake zargi da aika laifuka daban-daban a jihar cikin watanni shidan shekarar da muke ciki ta 2021.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abiodun Alabi, ne ya bayyana hakan jiya Alhamis ta cikin wata sanarwa da ya fita ga manema labarai, mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar SP Ahmad Wakil.
Alabi ta cikin sanarwar ya ce rundunar ta samu korafe-korafe 221 na mutanan data kama tsakanin 8 ga watam Maris zuwa watan Agustan da muke ciki.
Ya kuma ce mutanan da aka kama ana zargin su da aikata laifuka daban daban da suka hadar da na garkuwa da munate da fashi da makami da cin zarafin kananan yara da dai sauran laifuka.
You must be logged in to post a comment Login