Coronavirus
Sama da mutum 2000 aka yiwa gwajin cutar Covid-19 a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce mutum 2060 aka yiwa gwajin cutar Coronavirus tun daga lokacin da ta bulla a jihar zuwa yanzu.
Gwamna Alhaji Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Dutse.
Gwamnan yace cikin wancan adadi an samu mutane 283 da suka kamu da cutar inda tuni mutane 122 suka warke aka kuma sallae su yayin da mutum 8 suka rasu sakamakon cutar.
Kan cigaban da ake samu game da yadda ake yaki da cutar gwamnan ya yabawa kwamatin yaki da cutar da kuma al’ummar jihar kan irin kokarin da kowanne bangare yayi.
Gwamna Badaru ya ce, tabbas al’ummar jihar sun bada hadin kai, ta wajan sanar da kwamati duk wanda suka gani da alammomin cutar da aka fada da kuma matakan da gwamnati ta gindaya.
You must be logged in to post a comment Login