Labarai
Sanata Ajimobi ya maye gurbin Adams Oshiomhole a shugabancin APC
Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC ya naɗa tsohon gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi a matsayin shugaban riƙo na Jam’iyyar a matakin ƙasa.
Hakan ya biyo bayan hukunchin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi, da ya sake jaddada dakatarwar da aka yiwa shugaban Jam’iyyar na ƙasa Kwamaret Adams Oshiomhole ranar talata a Abuja.
Sakataren yaɗa labaran Jam’iyyar na ƙasa Mallam Lanre Issa-Onilu, shi ne ya tabbatar da wannan batu cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a daren Talatar nan.
Sanarwar ta ce jam’iyyar ta samu labarin hukunchin kotun ɗaukaka ƙara, da yake jaddada dakatarwar da aka yiwa Adams Oshiomhole daga babbar kotun birnin tarayya.
Sanarwar ta ci-gaba da cewa, sashen shari’a ya ba da shawarwari ƙarƙashin tsarin mulkin jam’iyyar ta APC sashe na 14.2 uku cikin baka, wanda ya fayyace cewa a yanayi irin wannan mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa Sanata Abiola Ajimobi daga shiyyar kudancin ƙasarnan, shi ne zai riƙe shugabancin jam’iyyar, sakamakon rashin shugabanta daga shiyyar da ya fito.
Yanzu haka dai labarin wannan dambarwa ta APC na cikin manyan batutuwan da suka fi ɗaukar hankalin ƴan Najeriya kuma ake muhawwara da cece-kuce kansa a shafukan sada zumunta irinsu Facebook da Twitter.
You must be logged in to post a comment Login