Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shamsu Dambazau zai samar da sabbin hanyoyin noma a Takai da Sumaila

Published

on

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumonin Takai da Sumaila a Majalisar wakilai ta kasa Shamsuddeen Bello Dambazau ya ja hankalin takwarorin sa wajen zage dantse akan matsalolin da suka dabaibaye al’ummar da suke wakilta.

Na gabatar da kudurin samar da tsaftataccen ruwan sha a yankin Sumaila, duba da matsalolin ruwan sha da mutanen yankin ke fama da shi don magance ta- Shamsuddin Dambazau

Shamsuddeen Dambazau ya kara da cewa, kasancewar Allah ya albarkaci yankin da yake wakilta da yalwar gonakin noma musamman na Dabino, inda ya ce tuni shiri ya yi nisa wajen kawo sabbin hanyoyin noman Dabino na zamani, don bunkasa tattalin arzikin su dana kasa baki daya.

Shamsuddeen Bello Dambazau ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai anan Kano.

Ya ce tun farkon shigar sa Majalisar nan ta tara, akwai kudurori da samu gabatarwa da suka shafi ci gaban al’ummar yankunan kananan hukumomin biyu.

Shamsuddeen Bello Dambazau ya kara da cewa, kasancewar sa mamba a kwamitocin noma da muhalli a Majalisar wakilai, ya maida hankali wajen bunkasa rayuwa da sana’ar manoman yankunan, baya ga samar da hanyoyin dakile ambaliyar ruwa da al’ummar wasu yankunan da yake wakilta suka fuskanta a shekarar da ta gabata.

       Wadansu magidanta sun karbi  Musulunci a garin Sumaila       

Kawu Sumaila: kafafun yada labarai abokan tafiyar mulkin dumukaradiyya ne

Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito dan Majalisar kananan hukumomin Takai da Sumaila Shamsuddeen Bello Dambazau ya bayyana cewa, a tsawon watanni bakwai da ya yi a zauren majalisar kasa, ya samawa dinbim matasa ayyukan yi masu matakin karatun Digiri kama daga aikin sojan ruwa dana kasa, da wasu a hukumar kashe gobara ta kasa, da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, da dai sauran su.

Shamsuddeen Bello Dambazau ya kuma bukaci cikakken goyon bayan al’ummar da yake wakilta, inda ya ce kofar sa a bude take wajen mika koken duk wata matsala da ta shige musu duhu don daukar matakin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!