Labarai
Shugaban Buhari ya bukaci al’umma su jajirce tare da nuna hakuri da juriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci al’ummar Nijeriya, da su kara jajircewa musamman wajen nuna hakuri da juriya da juna a zamantakewar rayuwa.
Wannan na cikin sakon taya al’ummar musulmi murnar bikin Sallah karama da shugaban ya aike wa ‘yan Nijeriya, bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan na bana, inda ya yi fatan dacewa da rahamar Ubangiji.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam garba Shehu ya fitar, ta rawaito shugaba Buhari na yabawa bisa yadda aka gudanar da babban zaben kasa na bana lami lafiya, yana mai bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara da ya cimma a mulkinsa.
You must be logged in to post a comment Login