Labarai
Siyasar Kano: An ja layi tsakanin Sha’aban da Ganduje
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar birnin Kano Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya caccaki gwamnatin Kano.
Cikin wani faifan bidiyo mai daƙiƙa hamsin da tara ya nuna Ɗan majalisar na sukar wasu tsare-tsaren gwamnatin Kano.
Sha’aban Sharaɗa ya ce, “Duka wani wuri da ya rage nan gaba da za a yiwa al’umma hidima ana sayar da shi, a kama makaranta a yanka a ce an ba wa wane”.
Ya ci gaba da cewa “A samu asibiti a yanka a ba wa wane, a samu masallaci a yanka a ce an bai wa wane, a samu hanya, maƙabarta a yanka ace an ba wa wane”.
“Me ake so? Me za a yi? Ina za ayi da duniya? Wallahi tallahi duk wanda ya sauraramin baya ƙaunar Allah”.
“Mun ja su ma su ja, mu ga wanda zai fi shan wahala” a cewar Sha’aban.
Karin labarai:
Siyasar Kano: An ja layi tsakanin Sha’aban da Ganduje
Siyasar Kano: Ko Baffa Bichi ya ƙwace takarar Abba Gida-Gida?
Sai dai tuni gwamnatin Kano ta yi martani ta bakin tsohon mai bai wa gwamna shawara kan al’amuran jama’a kuma ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar birni Fa’izu Alfindiki.
A cikin wani saƙon murya da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce, shi uban gidan Sha’aban ne a siyasa.
Alfindiki ya ce, “A siyasa ni ba sa’an ka ba ne, ni uban gidanka ne, ni na karantar da kai siyasa, ni na taimake ka a siyasa”.
“Ni nake binka bashi a siyasa, sauran waɗanda ke ƙasa da ni su ne sa’anninka a siyasa, amma Allah ya ɗaukaka ka, Allah ya daraja ka baka riƙi darajarka da muhimmanci ba”.
Yanzu haka dai al’umma na ta bayyana ra’ayoyinsu a kai musamman a kafafen sada zumunta.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke shirin zaɓen ƙananan hukumomi wanda tsagin masu hamayya suka ƙauracewa.
Ku kalli bidiyon na Sha’aban Sharada.
You must be logged in to post a comment Login