Labarai
Siyasar Kano: PDP ta dakatar da Al’amin Little
Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon ɗan takarar gwamnan Kano Ibrahim Al’amin Little na tsawon wata guda.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Nassarawa Sulaiman Mustapha Mainasara shi ne ya sanar da hakan ga Freedom Radio.
Mainasara ya ce, shugabancin mazaɓar Tudunwada ne ya aike musu da takardar dakatarwar bisa zarginsa da aikata laifukan da suka saɓa da kundin tsarin mulkin jam’iyya.
Ana zargin Little da tsame kansa daga al’amuran jam’iyya sannan ya kai jam’iyyar ƙara kotu, ba tare da yin ƙorafi ga jam’iyya ba, sannan ana zarginsa da yiwa jam’iyyar zagon ƙasa a cewar Mainasara.
Har kawo lokacin haɗa wannan rahoto Alhaji Al’amin Little bai ce komai ba a kai.
Karin labarai:
Kalaman Ɓatanci: PDP ta nemi Ali Baba ya bai wa Kwankwaso haƙuri
Siyasar Kano: Dalilan korar Kwankwaso daga PDP
Rikicin cikin gida abu ne da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a Kano, a makon da ya gabata ne tsagin Ambasada Aminu Wali ya sanar da korar tsohon gwamna Kwankwaso daga jam’iyyar.
Sai dai tsagin Kwankwaso ya yi watsi da korar da aka yi masa.
Yayin da ake rikicin shugabanci tsakanin ɓangarorin biyu, uwar jam’iyyar ta ƙasa ta ce tsagin Kwankwaso su ne halastattun shugabannin jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login