Da safiyar ranar Lahadi ne ƴan bindiga suka afkawa garin Lingyaɗi da ke ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Wasu mazauna garin sun ce ƴan bindigar sun yi awon gaba da mutane sama da hamsin.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce har yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.
Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Abubakar Justice Dauran ya shaida wa Freedom Radio cewa tuni jami'an tsaro suka bi sahun ƴan ta'addar cikin daji.
Talakawan jihar Zamfara dai na ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga.
Koda yake mahukunta na cewar suna iya ƙoƙarin su wajen kawo ƙarshen matsalar.
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.