Manyan Labarai
Takaddama : Mungono da Abba Kyari a zaman majilasar zartarwa ta kasa
Kasa da mako guda bayan takaddamar data kunno kai , tsakanin mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Janar Babagana Munguno mai ritaya da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Abba Kyari, akan zargin cin dunduniya da Abba Kyari kewa harkokin tsaro, an gan su tare yau a zaman majalisar zartarwa ta kasa yau Laraba da shugaba Muhammad Buhari ke jagoranta a fadar gwamnati.
Taron ya samu halartar manyan gaggan jami’an gwamnatin Shugaba Buhari, ciki har da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
Rahotanni sun tabbatar da cewar, shigar sa ke da wuya wajen gudanar da zaman majalisar , Babagana Munguno, ya zauna nesa kadan da shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati Abba Kyari, wanda Kujeru biyu suka shiga tsakanin su, sai dai daga baya Abba Kyari, ya yi nuni ga Babagana Mungono, daya matso kusa dashi inda ya amince tare da matsowa kusa Kujera daya tsakanin su maimakon biyu a baya.
Haka zalika , rahotanni sun tabbatar da cewar Kujera dayan da ke tsakanin nasu , gurin zaman shugabar ma’aikata ta kasa ce Misis Folasade Yemi-Esan.
Kano: Majalisar zartarwa ta kafa kwamitin kwararru kan kafafan yada labarai
Majalisar zartarwa ta amince da a gina sabbin makarantu 7 a shiyyoyin Najeriya
Kai tsaye: Kurun-kus majalisar dokoki ta Kano ta amince da sunayen kwamishinoni
A baya bayan nan dai , Janar Babagana Munguno mai ritaya , ya zargi shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Abba Kyari, da shiga sahro na Shanu a harkokin tsaro, wanda aka fitar da takardun zargin da yake masa , tare da cewar shi ya yi uwa ya yi makarbiya wajen hana shugaba Buhari canja manyan Hafsoshin kasar nan , duk da cewar wa’adin aikin su yayi, tare da koma bayan da ake samu ta fuskar tsaro a fadin kasar nan.
Al’umma da dama dai, na ganin Abba Kyari a matsayin wani mai karfin fada aji tare da juya shugaba Buhari, wanda hakan ya sa jama’a ke hasashen shi ke hana ruwa gudu wajen aiwatar da wasu aiyyukan da manufofin da shugaban yake dasu ,wanda al’ummar kasar nan suke zaton zai iya aiwatar wa tare da kai kasar nan ga gaci.
You must be logged in to post a comment Login