Coronavirus
Wadanda suka kamu da Corona sun kai 936 a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da samun karin mutane 13 dauke da cutar Covid-19 a jihar a ranar Laraba.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter a daren Larabar da misalin karfe 11:45 na dare.
Ma’aikatar lafiyan ta Kano ta ce an sallami karin mutum guda wanda ya warke daga cutar a ranar Laraban, sannan karin mutum 3 cikin masu dauke da cutar sun rigamu gidan gaskiya.
Yazuwa yanzu adadin masu dauke da cutar a Kano sun kai 936.
Mutane 135 daga ciki an sallame su bayan da suka warke sarai daga cutar.
41 daga ciki kuma sun rigamu gidan gaskiya.
Yanzu haka dai masu fama da Corona 760 ne ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake Kano.
A ranar Alhamis dinnan ne gwamnatin Kano tace zata shiga zagaye na biyu na rabon tallafin rage radadin dokar zama gida kan Corona ga mabukata.
Wakiliyar Freedom Radio a fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta rawaito mana cewa a ranar Alhamis din ne ake sa ran gwamna Ganduje zai bude cibiyar daukar samfurin gwajin masu cutar Corona a unguwar Sabon Gari dake Kano.
You must be logged in to post a comment Login