Labarai
Wasu marasa tarbiyya, ba arabi ba boko ne ke juya akalar Kano – Hadimin Ganduje
Hadimin Gwamna Ganduje kuma tsohon Kwamishinan ayyuka na Kano, ya ce, wasu tantirai marasa ilimin addini da boko ne ke juya lamuran gwamnati da siyasar Kano.
Ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook Injiniya Mu’az Magaji Ɗan sarauniya ya ce, “Jahilci ba ado ba ne, illa ne ga rayuwa da ci gaban zaman lafiyar al’umma”.
A cewar sa, “Jiha kamar Kano mai PhD Gwamna mai ilimin boko da addini”.
Ya ci gaba da cewa, “Amma a ce wasu tantirai ba arabi ba boko su ne ke juya akalar lamuran mu a siyasa da rayuwa”.
Ƙarin labarai:
Ina fatan mutuwa ta zama silar sulhun Kwankwaso da Ganduje – Ɗan Sarauniya
Abdullahi Abbas bai cancanci shugabancin jam’iyya ba – Ɗan Sarauniya
Wannan magana ta Ɗan Sarauniya ta haifar da kace-nace inda ya fara samun martani daga masu bibiyar shafin nasa.
Wani mai suna Deedat Assumaily ya ce “Mu’azu Magaji don Allah a dinga haƙuri”.
Shi kuma Hassan Cikinza Rano cewa ya yi, “Kuma wallahi yadda suka dama haka zaka sha”.
Sai Abubakar Inuwa Gama, da ya ce, “Win Win faɗa musu gaskiya”.
Ra’ayin Sani Aminu Ladan Ƙoƙi kuma cewa ya yi’ “Ƙwarai kuwa”.
A ranar Litinin ma dai Ɗan Sarauniya ya ƙalubalanci shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas da ya je ayi masa gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Batun da ya ɗauki hankulan jama’a musamman a kafafen sada zumunta, sai dai har kawo wannan lokaci ba a ji martani daga ɓangaren APC ba game da batutuwan da Ɗan Sarauniyar ke wallafawa.
A shekarar da ta gabata ne Gwamna Ganduje ya sauke shi daga Kwamishina, bayan wasu kalamai da ya yi a Facebook kan mutuwar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari.
Daga baya ne kuma, Ganduje ya sake naɗa shi a matsayin mai sanya ido kan aikin janyo bututun gas zuwa Kano.
You must be logged in to post a comment Login