Jigawa
Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Jigawa sun koka bisa rashin tsarin shugabanci
Wasu ‘yan majalissar dokokin jihar jigawa guda sun ce tsana da kuma rashin iya shugancin majalissar yasa aka cire su, daga shugabancin kwamatoci.
Tsohon shugaban majalissar dokokin jahar jigawa Isah Idris Gwaram ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da suka kira, a madadin ‘yan majalissar da lamarin ya shafa.
Isah Gwaram yace wannan mataki da aka dauka, ya sabawa doka, domin ba abi hanyar da dokar majalissar ta shimfida ba kafin zartar da haka.
Kan hakan ne ma yace zasu zauna da lauyoyin su don ganin irin matakin daya dace su dauka don kwatar hakkin su.
A yayin zaman majalissar dokokin jihar jigawa na ranar alamis din nan ne shugaban majalissar Idris Garba Jahun ya sanar da cire yan majalissar su hudu daga shugabancin kwamatocin da suke yi.
Kakakin majalissar yace hakan dai ya faru ne sakamakon raahin isasshen kudin gudanarwar majalissar, sakamakon cutar COVID-19, hujjar da tsohon kakakin yace ba gaskiya bace, domin ba a ragewa majalissar koda sisin kwabo ba na gudanarwa.
Dama dai an dade ana zaman doya da manja a majalissar tsakanin bangarorin biyu.
You must be logged in to post a comment Login