Labaran Wasanni
Ya zama dole Rohr ya jagoranci Super Eagles yin nasara – NFF
Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta yi kira da mai horar da kungiyar Super Eagles Gernot Rohr da ya yi duk mai yihuwa na ganin tawagar ta yi nasarar doke jamhuriyar Afrika ta tsakiya a wasan da zasu fafata a birnin Douala na kasar Kamaru a ranar Lahadi.
Wannna na zuwa ne bayan da Super Eagles tayi rashin nasara daci daya da neman a wasan farko da suka fafata a ranar Alhamis a jihar Lagos.
Shugaban hukumar ta NFF kuma mamba a hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA Mista Amaju Melvin Pinnick ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa da shugaban hukumar ya fitar.
Ta cikin sanarwar Pinnick ya ce ” hukumar NFF da gwamnatin jihar Lagos sunyi duk abin da ya kamata wajen bawa kungiyar goyan baya da kuma dukanin abin da suke bukata, amma sai gashi wasan ya zo mana da bazata domin kungiyar tayi rashin nasara,”
“Ma tuka nayi namaki da kuma jin babu dadi bayan ‘yan wasan mu Wilfred Ndidi da Oghenekaro Etebo da kuma Alex Iwobi ke fama da rauni, sai dai ina kira da mai horar da kungiyar da yayi duk abin da ya dace domin samun nasarar kungiyar wanda kuma zamu cigaba da yiwa tawagar fatan samun nasara,” a cewar Pinnick.
Najeriya dai itace ke jagorantar rukunin na C da maki shida, inda zata buga wasa na gaba da Jamhuriyar afrika ta tsakiya a ranar Lahadi a kasar Kamaru.
You must be logged in to post a comment Login