Addini
Yadda aka yi jana’izar sarkin Biu da safiyar yau Talata
Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da mutuwar sarkin Biu, Mai Umar Mustafa Aliyu a safiyar yau.
Kwamishinan yada labarai da raya al’adu Alhaji Babakura Abba-Jato ne ya tabbatar da mutuwar ta sa, ta cikin sanarwar da ya fitar.
Marigayi sarkin na Biu ya hau kan karagar mulkin tun a shekarar ta Alif darin tara da tamanin da tara zuwa bana.
Marigayi Mai Umar ya rasu yana da shekaru tamanin a duniya.
Kafin rasuwar ta sa dai ya taba rike mukamin dagacin garin Biu a shekarar 1975 kafin daga bisani ya zama sarki.
An gudanar da jana’izar sa da safiyar yau Talata
Allay ya jikan sa idan ta mu tazo ya sa mu cika da Imani.
You must be logged in to post a comment Login