Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan bindigar da suka tsere daga wasu yankunan Nijeriya sun yiwa Birnin Gwari kawanya

Published

on

Kwanaki kadan bayan labarin cewa ‘yan bindigar da suka tsere daga wasu yankunan na kutsawa cikin garin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.

Mazauna garin sun ce tun daren ranar Alhamis ne ‘yan bindigar suka kewaye da garin na Birnin-Gwari tare da yin awon gaba da jama’a da dama.

Wata majiya ta ce, al’amarin ya faru ne a unguwar Gobirawa da ke cikin garin Birnin-Gwari da ke kusa da gidan talabinjin na kasa wato NTA Birnin-Gwari da ke da nisan sama da mita 500 daga sansanin sojin sama.

Tuni dai Majalisar Karamar Hukumar Birnin-Gwari ta yi gargadi ga mazauna yankin da su takaita zirga-zirga a daukacin masarautar Birnin-Gwari.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!