Coronavirus
Yan jarida sun samu horo kan aiki da Corona a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata cigaba da baiwa yan jaridu goyon baya musamman wajen kare kansu daga cutar Corona yayin gudanar da ayyukansu.
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar asabar lokacin gudanar da taron bita ga yan jaridu guda 100 akan yadda zasu kare kansu daga kamuwa daga Corona yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce ‘yan jaridu suna taimakawa a wannan yaki da akeyi da wannan cuta adon haka ya zama lallai su samu kariya daga kamuwa da cutar ta Corona.
Labarai masu alaka:
Da gaske za ayi gwajin maganin Corona a Kano?
Ganduje ya bude cibiyar killace mata masu Corona a Kano
Da yake jawabi shugaban kwamitin ministan lafiya kan cutar Corona a Kano Dakta Nasir Sani Gwarzo cewa yayi kasancewar yan jaridu suna cikin hatsarin kamuwa da cutar adon haka ya zama lallai a ilmantar dasu yadda zasu kare kansu.
Abbas Ibrahim shine shugaban kungiyar yan jaridu reshen jihar Kano ya ce wannan horarwa zata taimakawa yan jaridun wajen yin ayyukansu cikin kariya.
Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa jami’an lafiya daga fannoni daban-daban ne suka yi ta gudanar da makalolin kariyar kai ga yan jaridu daga cutar ta Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login