Labarai
‘Yan Najeriya za su sha mamaki kan zargin Magu – Garba Shehu
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Malam Garba Shehu ya ce ‘yan Najeriya za su sha mamaki ya yin da ake cigaba da bankado bayanai kan zargin cin hanci da ake yi wa dakataccen mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu.
Garba Shehu ya bayyana hakan ne a tattauanawar sa da gidan talabijin na Channels ta cikin shirin (Sunday Politics).
Har Ila yau Malam Garba Shehu ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan bincike zargin da ake yi wa Ibrahim Magu zai gabatar da rahoton sa akan haka ne ‘yan Najeriya su kwan cikin shiri wajen shan mamakin abun da rahoton ya kunsa.
Kakakin fadar shugaban kasa ya kara da cewar, ana girmama tare da martaba shugaban kasa Muhammadu Buhari a duniya wajen yaki da cin hanci da rashawa a saboda haka ‘yan Najeriya su sani cewa babu wanda ya fi karfin doka.
Labarai masu alaka :
Malami ya dakatar da daraktoci 12 a EFCC
Za a janye ‘yan sandan dake aiki a EFCC
Hukumar EFCC ta gano ma’aikatan bogi 1000 a jihar Kwara
Da aka tambayi Malam Garba Shehu kan mamakin da ‘yan Najeriya za su sha kan bayanan da za su fito bayan da kwamitin ya mika rahoton sa, Garba Shehu ya ce, kwamitin da mai shari’a Ayo Salami mai ritaya ke jagoranta, na shedawa shugaban kasa kan cigaban da ake samu kan bayanan da suka samu a zargin da ake yi wa Ibrahim Magu.
You must be logged in to post a comment Login