Jigawa
Yanzu-yanzu: Gwamnati ta bada umarnin rufe makarantu a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada umarnin rufe makarantun Firamare da Sakandiren jihar bakiɗaya.
Mai riƙon muƙamin babban sakataren ma’aikatar ilimi da kimiyya ta jihar Alhaji Rabi’u Adamu ne ya sanar da hakan da yammacin Talata.
Alhaji Rabi’u Adamu ya ce, rufe makarantun ya shafi makarantu gwamnati da ma masu zaman kansu.
Sai dai bai bayyana dalilin rufe makarantun ba.
Amma tuni al’umma suka fara bayyana mabanbanta ra’ayoyi inda wasu ke danganta hakan da sace ɗaliban Sakandiren Ƙanƙara a jihar Katsina.
Wasu kuma na alaƙanta hakan da dake ɓarkewar annobar Corona.
You must be logged in to post a comment Login