Labarai
Za mu yi amfani da na’urorin zamani yayin aikin Kidaya- NPC
Hukumar kidaya ta Nijeriya NPC, ta ce, za ta yi amfani da na’urori na zamani wajen gudanar da aikin kidayar jama’a da za a gudanar a bana, domin tafiyar da aikin dai-dai zamani.
Shugaban hukumar shiyyar Kano Ismail Alhassan Doguwa, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakiliyar Freedom Radio Hafsat Abdullahi Danladi.
Tattaunawar ta su dai, ta mayar da hankali ne wajen jin irin shirye-shiryen da hukumar ke yi na gudanar da aikin kidayar nan gaba kadan.
Ya ce, a bana aikin zai isa har zuwa sansanonin yan gudun hijira domin sanin adadinsu.
Ganawar da shugaban hukumar kidaya a jihar Kano Ismail Alhassan Doguwa na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin tarayya ta bayyana ranar uku ga watan Mayun bana a matsayin ranar da za a fara aikin kidayar jama’a da gidaje a fadin Nijeriya.
Rahoton: Hafsat Abdulllahi Danladi
You must be logged in to post a comment Login