Labarai
Zargin fyade : Kotu ta wanke wani matashi a Kano
Babbar kotun jiha wacce mai shari’a Dije Abdu Aboki ke jagoran ta, ta wanke wani matashi mai suna Saifullahi Haruna Kabo da ake zargin da aikata fyade ya yin da ta sallami shi.
A dai kwanakin baya ne ake zargin matashin Saifullahi Haruna Kabo da laifin hada baki da kuma laifin fyade, bayan kuma kotun ta gano ba shi da laifi.
Sai dai kafin wanke shi Saifullahi Haruna Kaboa ya kwashe tsawon shekaru uku a gidan gyaran hali.
Bayan da mai shari’a Dije Abdu Aboki ta wanke shi da safiyar yau wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya zanta da matashin yana mai bayyana jin dadin sa akan yadda kotun ta gane bashi da laifi kan zargin yi wa wata yarinya fyade.
Kotu a Kano ta aike da Kansila gidan gyaran hali
Kotu ta yi sammacin shugaban KAROTA
“Ya na mai cewa, kotu tayi min adalci ta duba tayi bincike ta gane mai laifi, kuma da ba ni da laifi ta sake, nayi matukar godiya
Ya kuma ce, shekaru ukun da nayi a gidan gyaran hali, na koyi darussa da dama, dole ka tsaya ka gina rayuwar ka, idan kana yin abun da ba daidai ba ne ka gyara, kuma kurkuku gida ne na gyaran hali, idan ka so ka gyara”.
You must be logged in to post a comment Login