Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Ƴan soshiyal midiya na tsokaci kan tuhumar kisan kai ga tsohon soja

Published

on

Masu amfani da kafafen sada zumunta na ci gaba da yin Alla-wadai kan wani tsohon soja da aka kama bisa zargin yin garkuwa da wanin ƙanƙanin yaro.
Ƴan sanda sun cafke tsohon sojan mai suna Sani Galadima ne a unguwar Badarawa da ke Kaduna, bisa zargin yin garkuwa da ɗan maƙocinsa tare da hallaka shi bayan ya karɓi kuɗin fansa.

Rahotanni sun ce, Galadima ya yi amfani da wani matashi wajen satar ƙaramin yaron, sannan suka nemi kuɗin fansa.
Mahaifin yaron Alhaji Kabiru Magayaki ya biya kuɗin fansar har miliyan biyar.

Sani Galadima na cikin waɗanda suka riƙa zuwa har gida domin yin jaje ga mahaifin yaron.
Waɗanda ake zargin sun shaidawa ƴan sanda cewa, sun hallaka yaron tare da jefa shi a wata magudanar ruwa da ke Kano, saboda ya gane ɗaya daga cikin su.

Ƙarin Labarai:

Ko ‘Da na ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da shi ba zan basu kudin fansa ba – El-Rufai

Yanzu-yanzu- An sake sakin daliban kwalejin Afaka da masu garkuwa da mutane suka sace

Me ya sa masu amfani da kafafen sada zumunta suka kaɗu da afkuwar lamarin?

Sani Galadima ɗaya ne daga cikin fitattun masu amfani da kafafen sada zumunta, inda lokaci zuwa lokaci yake nuna takaicin sa kan matsalolin tsaro.

Mabiyan sa a kafafen sada zumunta sun nuna takaicin su kan faruwar lamarin, musamman ma bayan fitar wani bidiyo da Sani Galadiman ya ke bayanin yadda ya aikata hakan.
Ku kalli bidiyon a nan.

ASP. Muhammad Jalige shi ne mai magana da yawun ƴan sandan jihar Kaduna ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin.

Ya ce, waɗanda ake zargin suna hannun su inda suke ci gaba da bincike.

Yanzu haka dai tuni jama’a suka shiga yin tsokaci game da lamarin..

Ga wasu masu amfani da kafafen sada zumunta da suka tsokaci a kai.

Gaskiya SA Galadima korarren Soja yayi asara wallahi.

Posted by Kabiru Ado Muhd on Saturday, May 1, 2021

Wannan shine Azzalumin kidnapper da aka kama yau a Badarawa S.A. GALADIMA korarren soja an taba kama shi da laifin sata…

Posted by Haruna Dutsen-wai on Friday, April 30, 2021

After collecting as ransom a sum of five million naira (₦5,000,000) from his neighbour, a child of whom he kidnapped in…

Posted by Alhaji Musa Ashafa Jr. on Friday, April 30, 2021

The face of inhumanity. The face of betrayal. The face of cruelty. The face of filthy kidnapper. Allah ya isa

Posted by Yakubu Musa on Saturday, May 1, 2021

Gashi Rungume Da Nashi.
Amma Yayi Kidnapped Kuma Ya Kashe Diyansu.

SA GALADIMA

Allah Ya kara Tunama Ire Irenka Asiri.

Posted by Mukhtar Elduniya Shinkafi on Saturday, May 1, 2021

Allah ka shiga tsakanin mu da marasa imani. Ka kare mu da yaran mu, iyali, yan uwa da abokan arziki.

Posted by Isma’il M. Ahmad on Saturday, May 1, 2021

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!