Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da ya sanya NECO ba ta saki sakamakon ɗaliban Kano ba

Published

on

Tun a ranar 13 ga watan Janairun da muke ciki ne hukumar shirya jarrabawa ta ƙasa NECO ta sanar da sakin sakamakon ɗalibai.

Yanzu kusan kwanaki goma kenan amma ɗaliban da ke karatu a makarantun Gwamnatin Kano sun gaza samun sakamakon su.

Da zarar ɗaliban sun shigar da bayanansu a shafin hukumar domin neman samun sakamakon, sai shafin ya basu amsa da cewa, “ba a saki sakamakon su ba saboda rashin biyan kuɗin jarrabawar”.

Ku kalli saƙon da ɗaliban ke samu ida sun duba jarrabawar.

Wata ɗaliba da ke karatu a ɗaya daga makarantun Gwamnatin Kano da muka zanta da ita, ta ce lamarin yana damunta ƙwarai.

Ta ce, “Ina da ƙawaye waɗanda suke makarantun kuɗi, duk sun dubo sakamakon su, amma mu namu yaƙi, na ƙagu na ga abin da na samu domin na san shirin da zanyi a gaba”.

Shi ma wani ɗalibi cewa ya yi, “Sau biyar ina zuwa duba jarrabawata daga ranar Larabar da aka sanar zuwa wannan Larabar amma ba a da cewa”.

“Muna roƙon Gwamnatin Kano da ta taimaka a sakar mana sakamakon jarrabawar nan”.

Karin labarai:

Ganduje ya sanya hannu kan dokar ilimi kyauta kuma dole a Kano

Muna goyon bayan ilimi kyauta kuma wajibi -sabon Sarkin Kano

Kan wannan batu dai Freedom Radio ta ziyarci ofishin hukumar NECO da ke Kano sai dai jami’an hukumar sun ce ba za su ce komai ba.

Amma sun bamu lambar jami’in yaɗa labaran hukumar ta ƙasa Malam Aziz Sani.

Mun tuntuɓe shi inda ya ce, zai yi mana ƙarin bayani zuwa ranar Alhamis.

Mun sake tuntuɓarsa a ranar Alhamis ɗin amma ya ce, mu ƙara haƙuri zuwa ranar Litinin zai yi mana ƙarin haske a kai.

Sai dai Aziz Sani ya tabbatar da cewa, akwai jihohin da basu saki sakamakonsu ba saboda bashin kuɗin da hukumar take binsu.

Amma ya ce, bai zai iya rarrabe wa ko jihar Kano na cikin jihohin ba har sai zuwa ranar Litinin ɗin.

Mun tuntuɓi Kwamishinan Ilimi na Kano Malam Muhammad Sanusi Ƙiru.

Ya kuma ce, ba komai ya haifar da tsaikon sakin sakamakon ba, sai tsarin Gwamnatin tarayya na asusun bai-ɗaya saboda haka, sai an bi hanyoyin aiki na musamman kafin biyan kuɗin.

Ƙiru ya ce, a ranar Alhamis ɗin nan hukumar NECO ta aiko masa da takardar shirin biyan kuɗin, kuma tuni ya aika da ita zuwa ga ofishin Babban Akanta na Kano.

Ya ci gaba da cewa, A ranar Alhamis kuɗin za su isa ga NECO kuma, daga Jumu’a zuwa Litinin ɗalibai su saka rai da samun jarrabawar su.

Ɗalibai sama da dubu 29 ne Gwamnatin Kano ta ce, za ta biyawa kuɗin jarrabawar bayan da suka cika sharuɗan da ta sanya na samun darusa 5 a jarabawar Kwalifaiyin waɗanda suka haɗar da turanci da lissafi.

Tun a baya dai Gwamnatin Kano ta shelanta rungumar tsarin karatu kyauta kuma dole.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!