Manyan Labarai
An sake samun bullar cutar Coruna Virus karo na uku a kasar nan
Gwamnatin jihar Lagos, ta sanar da sake bullar cutar Corona Virus, a jihar bayan samun wata mata mai shekaru 30, da ke dauke da ita bayan dawowar ta kasar nan daga Ingila, sakamakon ziyarar kwana 10 da tayi a can.
Kwamishinan lafiya na jihar Lagos, Akin Abayomi, ne ya bayyana wa manema labara a wani taron ‘yan jaridu da ya gudana a yau in da yace zuwa yanzu haka karo na uku ke nan da ka samu bullar cutar a jihar.
Akin Abayomi, ya kara dacewa matar wacce yanzu haka an killace ta, ta nuna alamun rashin lafiya na kamuwa da cutar ta Covid 19, da suka hada da tari, zazabi mai zafi da makamantan su.
Labarai masu alaka.
Hisbah ta gano maganin Coronavirus
Daliban Kano a Sudan sun nemi a dawo dasu gida saboda Coronavirus
Kwamishinan yace bayan kwakkwaran bincike an samu matar da kamuwa da cutar, wadda ita ce karo na uku da aka samu bullar cutar a jihar ta Lagos, da a yanzu haka ya tabbatar da cewar ministan lafiya na kasa Osagie Ehanire, na gudanar da taron manema labarai yanzu haka don karin haske akan lamarin.
Akin Abayomi, yace matar ta sauka a kasar nan ne, a birnin na Lagos ranar 13 ga watan Maris, an kuma killace ta daga cikin iyalanta, kasancewar ba wai ana zargin ta da cutar bane an tabbatar tana dauke da cutar.
Zuwa yanzu haka tana killace a Asibitin cututtuka masu yaduwa dake Yaba. Hakan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jihar ta Lagos, ta bayyana cewa mai duke da cutar da aka samu na biyu ya warke daga cutar.
You must be logged in to post a comment Login