Coronavirus
An sassauta dokar kulle a jihar Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar kulle ta lockdown, bayan an shafe tsawon watanni.
Gwamna Nasir El-Rufa’I ne ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatarwa al’ummar jihar, game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka kan dokar kulle.
Sai dai gwamnatin ta sanya dokar takaita zirga-zirga a jihar daga karfe takwas na dare zuwa karfe biyar na asuba.
A cikin jawabin nasa gwamna El-Rufa’I ya ce duk dan kasuwar da aka samu da saba dokar da aka gindaya za a dauki matakan da suka dace a kansa. Saboda haka za a bude kasuwanni sai dai da yarjejeniyar mutane zasu rika amfani da takunkumin rufe fuska da baki, wanke hannu a kowanne lokaci, amfani da sinadarin da ke kashe kwayoyin cuta da dai sauran su.
Ma’aikata zasu rika fita aiki daga karfe tara na safe zuwa karfe uku na yamma. Sannan za a rika bude majami’u sau daya kawai a sati, wato ranar Lahadi, yayinda za a rika bude masallatai kuma ranar Juma’a.
Direbobin mota zasu rika daukar fasinja biyu maimakon uku ko hudu da ake dauka a layin kujera guda.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a bude manya da kananun shaguna, har ma da masu hada-hadar kayan miya.
“Muna kira ga mazauna jiharmu da su yi biyayya ga dokokin da muka gindaya, zamu janye wannan mataki da muka dauka matsawar aka yi mana karan-tsaye, abinda za muyi shine zamu kara sanya dokar zama a gida dole”. Inji El-Rufa’i
A cewar gwamnan cutar Covid-19 ta bankado kalubale da dama da suka yi katutu a ma’aikatu da kuma bangaren kiwon lafiya, saboda haka gwamnati za ta yi dukkan mai yuwuwa don ganin ta shawo kan matsalolin.
You must be logged in to post a comment Login