Coronavirus
An yi wa Sule Lamido gwajin Coronavirus
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da wasu makunsantansa sun kai kansu cibiyar gwajin cutar Covid-19 da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano, biyo bayan mu’amala da ake kyautata zaton sun yi da mai dauke da Cutar a nan Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Sule Lamido da ma dinbin jama’a sun halarci wani taron janaiza a Unguwar Koki a ranar alhamis din da ta gabata, inda mai dauke da cutar ya yi mu’amala da mutane da dama.
LABARAI MASU ALAKA
Covid -19: Shugaba Buhari zai yi jawabi akan Corona
Ganduje ya tabbatar da bullar cutar Corona a Kano
Da Dumi-Dumi: An samu bullar Corona Virus a Kano
Kwamitin kai ta kwana kan yaki da cutar Covid-19 na Jihar Kano ne ya aikewa tsohon gwamnan da ma wasu mutane sako da ke shawartarsu da su je a gwada su don sanin matakin lafiyarsu.
Sakataren kwamitin wanda kuma shi ne daraktan sashen kula da lafiyar al’umma na ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano Dakta Imam Wada Bello, ya tabbatarwa Freedom Radio da yammacin yau cewa ba wai Alhaji Sule Lamido kadai suka gayyata ba, har ma da wasu mutanea nan Kano da ake kyautata zaton sun yi mu’amala da mai dauke da cutar ta Covid-19 a nan Kano.
You must be logged in to post a comment Login