Labarai
Atiku ya nemi CBN da kada su ƙara wa’adin sauya tsoffin kuɗi
Ɗan takarar Shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya roƙi Babban Bankin Ƙasa CBN da kada ya ƙara wa’adin 10 ga Fabrairun da muke ciki na ci gaba da sauya tsoffin kuɗi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Atiku Abubakar na cewa, wasu ƴan siyasa na son amfani da damar ƙara wa’adin don yin maguɗin zaɓe.
Ya kuma roƙi CBN da ya duba yiwuwar ƙara yawan takardun sabbin kuɗin domin ragewa jama’a raɗaɗin rashin kuɗi a hannu, musamman ga mutanen da ke yankunan karkara.
Shugaban CBN dai ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu domin daina amfani da tsoffin kuɗi a tsakanin jama’a.
CBN ya ce, yana aiwatar da tsare-tsaren sauya fasalin kuɗi da taƙaita hada-hadar kuɗi a hannu domin sake farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.
LABARAI MASU ALAKA:
Wasu cikin jami’an gwamnati a fadar Villa na yi wa Tinubu zagon kasa- El-rufai
Ba a haifi Atiku a Najeriya ba, bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba – Malami
You must be logged in to post a comment Login