Kiwon Lafiya
Covid-19: An fara rufe makarantun Islamiyya a Kano
Hukumar makarantar Islamiyya ta Tahfizul Qur’an dake unguwar Daneji a Kano ta rufe makarantar a ranar Asabar saboda fargabar annobar Coronavirus.
Sakataren makarantar Dakta Ahmad Abdullahi Ibrahim Daneji, ya shaidawa Freedom Radio cewa, sun baiwa daliban makarantar hutu ne ganin yadda gwamnati ta bada umarnin rufe sauran makarantun jihar.
Dakta Ahmad Daneji ya ce sun shaidawa daliban makarantar cewa su zauna a gida na tsawon mako biyu su cigaba da yin addu’o’I, da kuma bin ka’idojin da jami’an lafiya suka bayar.
“Sannan mun sanar da su cewa idan Allah ya sa an samu sauyi, gwamnati ta sanar da wata sanarwa da ta nuna za a cigaba da gudanar da al’amuran yau da kullum, to dalibai su dawo mu cigaba da karatu” a cewar Dakta Daneji.
Karin labarai:
Covid-19: An dakatar da kwallon kafa a Kano saboda Coronavirus
Musulmai sun yi taron addu’a kan Coronavirus a Kano
Makarantar Tahfizul Qur’an Daneji, na cikin manyan makarantu dake da yawan dalibai a kwaryar birnin Kano.
Idan baku manta ba, tuni gwamnatin jihar Kano ta bi sahun sauran gwamnatocin jihohin Arewa cin kasar nan wajen rufe daukacin makarantu saboda fargabar cutar Coronavirus.
You must be logged in to post a comment Login