Labaran Wasanni
Covid-19: Ba kungiyar da zata biya kudin gwaji -Shehu Dikko
This is a Story in the imagination of the writer anyway as LMC or NFF or Sport Ministry never said so or discussed this with anybody or proposed for any club to pay for any testing when and if the need arrises talkless of doing testing before every match
— Shehu Dikko (@ShehuDikko) June 9, 2020
Shugaban hukumar shirya gasar Lig ta kasa (LMC )Shehu Dikko, ya musanta rade radin da ake na cewar kungiyoyin firimiya zasu biya kudin gwaje –gwajen ‘yan wasan su da sauran mukarraban tawagar su na cutar Corona da zarar an dawo gasar.
Shehu Dikko, wanda shi ne mataimakin na biyu na hukumar kwalon kafa ta kasa NFF, ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, jim kadan bayan da rade radin rahotanni suka fita na cewar kungiyoyin gasar guda 20, su zasu biya kudin gwaje gwajen, ‘yan wasan nasu har naira milayan 50, in an dawo cigaba da gasar.
Shehu Dikko, ya kara dacewa labarin duk shaci fadi ne, kasancewar hukumar gasar lig ta kasa LMC da kuma ta kwallon kafa ta kasa NFF, da ma’aikatar wasanni ta kasa basu tattauna hakan ba ko yiwuwar yin hakan ga kowa, ko wata kungiya ballantana ta kai gwaji.
Labarai masu alaka.
‘Yan wasan cikin gida zasu fara wasa a Super Eagles-Shehu Dikko
Covid -19 Ba za’a rage albashin ‘yan wasan firimiya ta kasa ba
A baya dai ministan wasanni Mista Sunday Dare, ya bayyana cewar ko an dawo wasannin ba za’a bar ‘yan kallo su shiga kallon wasannin ba.Kawo yanzu dai ba san yadda zata kasance ba wajen tsare tsaren dawowa gasar ba.
Gasar Firimiyar ta kasa kamar sauran takwarorin ta na kasashen duniya ta samu tsaiko, kasancewa bullar annobar. Kawo yan zu haka kungiyar kwallon kafa ta Plateau United, ke jagorancin teburin gasar bayan wasanni 25,da maki 49, ya yin da Rivers ke biye mata a baya sai Lobi stars dake a matak na uku.
You must be logged in to post a comment Login