Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

COVID-19: Me ke faruwa a kasashen duniya?

Published

on

AN KULLE WASU SASSA A BIRNIN BEIJING SABODA CORONAVIRUS

Hukumomi a Beijing na kasar China sun sanya dokar kulle a wasu sassa na birnin bayan da aka samu rahoton cewa mutum shida sun kamu da cutar Coronavirus.

SAMA DA MUTUM 300,000 AKA TABBATAR SUN KAMU DA CORONAVIRUS A INDIYA

Indiya ta fitar da rahoton sabbin alkaluman da aka samu na masu dauke da cutar numfashi, yayin da kasar ta shiga wani mummunan yanayi na adadin wadanda ke dauke da cutar da suka tasamma 300,000.

COVID-19: BRAZIL TA DOKE KASASHEN AMURKA DA INGILA A YAWAN MUTANEN DA SUKA MUTU

Kasar Brazil ta zamo kasa ta biyu a duniya da ke da yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar Covid-19, inda yanzu haka mutum 41,828 suka mutu a kasar. Kamar yadda rahotanni suka tabbatar hakan ya nuna cewa adadin wadanda suka mutu a Brazil ya zarce na kasashen Amurka da Ingila.

Fiye da mutane miliyan 7.6 kawo yanzu aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Coronavirus a duniya, inda mutum 426,000 suka mutu, a cewar rahoton Jami’ar Johns Hopkins.

SHUGABAN CHILE YA TSIGE MINISTAN LAFIYA NA KASAR          

Shugaban kasar Chile Sebastian Pinera ya maye gurbin ministan lafiya na kasar Jaime Manalich a yayin ake suka game da alkalumman wadanda suka mutu sakamakon cutar Coronavirus.

Pinera ya ce babu wani katabus da Manalich wajen aiwatar da aikin lafiya, domin kare lafiyar ‘yan kasar ta Chile. Shugaba Pinera ya maye gurbinsa da Oscar Enrique Paris, wanda masanin ilimin kimiyya da aikin likita ne.

KASASHEN TURAI NA TATTAUNAWA KAN YADDA ZA A SAMAR DA RIGAKAFIN COVID-19

Kamfanin sarrafa magunguna na AstraZeneca na tattaunawa da kasashenJapan, Rasha, Brazil da China game da yarjejeniyar samar da maganin rigakafin cutar coronavirus, kamar yadda shugaban kamfanin ya sanar.

Hukumar Kula da Lafiyar Jama’a da Kayayyakin Kiwon Lafiya(MHRA) ta Burtaniya ta amince da fara gwajin kashi uku na allurar bayan binciken da aka yi ya nuna inganci da kuma sahihancin sa, in ji Babban Daraktan hukumar Pascal Soriot a yayin wata hira da manema labarai.

Hakazalika kasashen Itliya da Jamus da Netherlands sun ƙulla yarjejeniya da kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca domin samar da maganin riga-kafi ga al’umarsu.

ZA A FARA YIWA JEMAGU GWAJIN CORONA A THAILAND

Masana a kasar Thailand sun fara yi wa Jemagu gwajin cutar Cotronavirus yayinda ake fargabar barazana ce ga lafiyar al’umma.

Samfurin a kalla jemagu 300 za a karba daga wani kogo da ke yankin Chanthaburi a kudu maso gabashin Thailand.

FARANSA ZATA BUDE IYAKARTA RANAR 1 GA WATAN YULI

Kasar Faransa ta ce zata budewa kasashen da ke wajen yankin Schengen iyakarta daga ranar 1 ga watan Yuli, in ji sanarwar ministocin cikin gida da harkokin kasashen waje.

Ministan Harkokin Waje Jean-Yves Le Drian da Ministan Harkokin Cikin Gida Christophe Castaner sun ce sake bude Faransa za ta yi daidai da sauran kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai, wanda ya ba da shawarar cewa kungiyar ta sake bude wa wasu kasashe a yankin Balkans daga ranar 1 ga Yuli.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!