Addini
Idan za’a magance ta’addan ci a Nigeria sai an binciko ‘yan ta’addan dake boye -Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci hukumomin tsaro a kasar nan da su binciko ‘yan bindigar da ba a san su ba.
Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci hakan ne ya yin taron shugabannin addinai da aka gudanar jiya Alhamis a birnin tarayya Abuja.
A ranar Talata ne Sarkin musulmi ya cika shekaru 65 a Duniya
Sarkin Musulmin ya ce idan har hukumomin tsaro ba su yi gaggawar shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan ba, hakan zai iya haifar da gagarumar matsala a nan gaba.
Ya kuma ce abin da matukar mamaki ta ‘yadda ‘yan ta’adda ke kutsawa garuruwa a kasar nan suna kashe mutane ba tare da an kama su ba.
You must be logged in to post a comment Login