Labarai
Firaministan Sudan ya maye gurbin wasu ministocin kasar
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya maye gurbin ministocin kudi, da na kasashen waje, da na makamashi da na kiwon lafiya da kuma wasu manyan ministocin uku, a wani bangare na shirin sake aiwatar da sauye-sauye.
Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce sauye-sauyen na zuwa ne sakamakon bullo da wasu matakai da take ganin za su kawo gyara a sha’anin mulkin kasar.
Mahukuntan kasar dai sun ce sauyin ya zo a bazata, sakamakon cewa ‘yan kalilan ne ke tsammanin maye gurbin Ibrahim al-Badawi, wanda a matsayinsa na ministan kudi ya jagoranci kokarin kawo karshen matsin tattalin arzikin kasar wadda ke fama da rikice-rikicen, inda ya yi hulda sosai da masu ba da tallafi daga kasashen waje.
Heba Ahmed Ali, shine wanda zai maye gurbin Al-Badawi wanda wani babban jami’in ma’aikatar kudi ne kamar yadda sanarwar gwamnatin ta ce.
You must be logged in to post a comment Login