Labarai
Harin kwanton bauna ya kashe sojoji da dama a jihar Katsina
Harin kwanton bauna na wasu ‘yan bindiga ya kashe sojoji akalla 16 tare da jikkata 28 daga cikinsu a jihar Katsina.
Dakarun rundunar ta musamman su na kan hanyar zuwa garin Shimfida a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, a lokacin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta, kamar yadda wata majiya ta bayyana daga rundunar.
Daga cikin sojojin da harin ya rutsa da su akwai me mukamin manjo, kyaftin, laftanal, kamar yadda majiyar daga rundunar sojin ta tabbatar. Amma mutum biyu daga cikin maharan sun samu raunuka a lokacin da ake musayar wuta.
Ko da yake har yanzu rundunar sojin Najeriya bata magantu a kan al’amarin ba.
Katsina inda nan ce mahaifar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta kasance daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Sama da mutum 2,000 ne suka mutu a jihar Katsina, yayinda kauyuka sama da 500 suka lalace, kuma fiye da mutum 33,000 ne suka rasa muhallansu, a cewar rahoton kungiyar rajin samar da zaman lafiya ta yammacin na 2020 da ta fitar.
Shugaba Buhari, ya yi alkawarin tura manyan sojoji yankin domin kawar da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, bayan da al’ummar jihar Katsina suka yi zanga-zangar nuna fushinsu kan yadda al’amuran tsaro ke tabarbarewa a yankin.
You must be logged in to post a comment Login