Labarai
Hukumar EFCC ta mikawa jami’ar Dutsinma motocin sata
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC , reshen jihar Kaduna ta mika motoci guda hudu da ta kwato daga hannun wasu hukumomin jami’ar tarayya ta Dutsinma dake jihar Katsina ga hukumomin jamia’ar.
Mai magana da yawun hukumar Mr Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja , ya ce an samo motocin ne biyo bayan takarda da ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya fitar.
Mr Uwujaren yace ministan yana zargin wasu daga cikin shugabannin jamia’ar da biyan kansu wasu miliyoyin kudade a matsayin alawus , tare da sanya kansu wasu ayyukan da ake zarginsu da cin hancin da rashawa ta hanyar amfani da bankin First bank.
Wasu daga cikin laifukan da ake zarginsu da shi sun hadar da almundahana wajen sayo kayayyakin aiki da kara kudadensu ta hanyar kara farashi, da kuma baiwa wasu kwangiloli ta hanyar hadin baki da kara kudade.
Hukumar EFCC ta cafke masu kamfanin boge da bindigu a Kano
Kayayyakin da aka kwato sun hadar da wasu motoci Toyota corolla guda biyu mai dauke da lamba FUDMA 51F -03FG da FUDMA 51F-05FG, sai wata Toyota Land Cruiser ZTRJ150L mai dauke da lamba FG 668 – E45 da kuma Toyata Camry XLE 205 da kuma ABC 601 LX.
Da yake mika kayayyakin, shugaban hukumar EFCC reshen jihr Kaduna Mailafia Yakubu ya ce an saki motocin ne biyo bayan bukatar jami’ar na sakar motocin.
Ya ce mika musu motocin na daga cikin irin ayyukan da hukumar