Labarai
Iftila’i: Sabuwar annoba mai hatsari ta ɓarke a Kano
Wata annoba ta ɓarke a unguwar Warure da ƙaramar hukumar Gwale.
Ana zargin annobar ta samo asali ne sakamakon amfani da ruwan wata rijiya da ke maƙabartar Ɗandolo.
Wata mata Siyama Muhammad da ta kamu da annobar ta yiwa Freedom Radio bayanin yadda ta kamu da ita.
Ta ce, “Bayan ta yi girki da ruwan da suka siya a wajen ƴan garuwa shikenan sai ta fara aman majina da fitsarin jini, sai kuma zazzaɓi da ciwon kai da riƙewar gaɓoɓi”.
Labarai masu alaka:
Annobar Corona ba ta tsayar da ayyukan mu ba – NITDA
Limami: Sakacin koyarwar addinin musulinci shike kawo annoba
Yanzu haka dai tuni aka garzaya da mutane 17 zuwa asibitin lura da mafitsara na Abubakar Imam.
Shugaban asibitin Dr. Atiku Ado Muhammad ya bayyana wa Freedom Radio cewa, wannan annoba ce kuma ta wuce batun mafitsara la’akari da bayanan da marasa lafiyar suka yi.
Saboda haka ya ce, za su tura su asibitin koyarwa na Aminu Kano domin ci gaba da bincike da ba su agajin gaggawa.
Mun tuntuɓi Kwamishinan lafiya na Kano, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa sai dai ya ce, zai yi mana bayani nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login