Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ana zargin Malama da hallaka ɗalibinta ɗan aji 2 a Nursery

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge a nan Kano ta rufe Makarantar Assalam da ke unguwar Kwaciri.
Hakan ya biyo bayan zargin wata malamar makarantar da yin ajalin wani ƙaramin yaro ɗan aji biyu a ɓangaren Nursery na makarantar, a ranar Talata.

Shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Ibrahim Muhammad Shehi ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.
Yana mai cewa, bayan rufe makarantar an kuma jibge jami’an tsaro a unguwar domin tabbatar da zaman lafiya.
Rahotanni sun ce, bayan faruwar al’amarin matasan unguwar sun yi ƙoƙarin ɗaukar doka a hannu.

Ƙarin Labarai:

Wata cuta da ba a kai ga gano asalinta ba ta hallaka mutane 6 a Kano

‘Ƴan bindiga sun hallaka mutane biyu a Kano

Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin.
Ya ce, tuni rundunar ta shiga bincike har ma an gayyaci malamar da ake zargi da kuma masu makarantar.

 

A nata ɓangaren mahaifiyar yaron ta shaida wa Freedom Radio cewa, daman malamar ta jima tana dukan ɗan nata.
Sannan abokan sa ɗalibai sun shaida mata cewa dukan malamar ne yayi ajalinsa.
Ta ci gaba da cewa, babban abin takaicinta shi ne yadda malamar ta bi ta da baƙaƙen maganganu a lokacin da ta zo ta’aziyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!