Labarai
Likitoci za su shiga yajin aiki a Legas
Kungiyar likitoci ta Jihar Lagos ta ce daga gobe litinin za ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku, bayan da gwamnatin jihar ta gaza cika ma ta alkawuran da ta dauka na biya mata wasu bukatunta.
Shugaban kungiyar Dr. Oluwajimi Sodipo ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai ranar Lahadi a Lagos, bayan karewar wa’adin da suka baiwa gwamnatin.
Dr Oluwajimi Sodipo ya ce tun a ranar 27 ga watan Yunin da ya gabata ne suka cimma matsayar karawa gwamnatin wa’adin makonni biyu domin biya musu bukatunsu akalla kashi 70 cikin 100, bayan karewar na kwana 21 da suka bayar tun farko, wanda kuma hakan ba ta samu ba.
Karin labarai:
Legas ta koka kan yawan samun masu Corona a jihar a kullum
Wani gini mai hawa uku ya ruso a Legas
Daga cikin bukatun na su akwai neman dai-daita albashinsu da na likitocin da ke aiki karkashin gwamnatin tarayya, da biyan bashin albashin watanni biyu da likitocin da ke cibiyoyin killace masu fama da cutar Covid-19 a Jihar ke bin gwamnatin.
Sai kuma batun karancin likitocin da ake fama da shi a Jihar, wanda kungiyar ta bukaci a kawo karshen matsalar, da kuma bunkasa walwalar likitocin.
You must be logged in to post a comment Login