Labarai
Majalisar dattijan Najeriya ta dawo daga hutu
‘Yan majalisar sun yi zama na dan wani lokaci, kafin daga bisani majalisar ta yanke shawarar dage zamanta na ranar Laraba.
Sanarwar ta biyo bayan wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Abdullahi Yahaya ya gabatar, inda ya ba da sanarwar mutuwar dan majalisar daga jihar Legas, Bayo Osinowo, wanda ya mutu a ranar 15 ga Yuni.
Mambobin majalisar sun gudanar da addu’o’I ga marigayin tare da zama ba tare da cewa komai na wasu ‘yan mintuna.
An kuma dakatar da zaman majalissar da sauran ayyuka, domin nuna girmamawa ga marigayin, bisa ka’idar majalisar dattawa.
Kudirin ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Enyinnaya Abaribe.
Sanata Osinowo wanda ya wakilci gundumar Legas ta Gabas a zauren majalisar ya mutu a wata cibiyar killace masu dauke da cutar Covid-19 da ke Legas, ya na mai shekarar 64.
You must be logged in to post a comment Login