Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya magantu a kan binciken Magu

Published

on

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya magantu kan binciken da ake yiwa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Wata sanarwa da babban mataimakin shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana dalilan da suka sanya fadar shugaban kasa ta amince a dakatar da Ibrahim Magun daga kujerarsa.

Sanarwar ta ce dakatar da Ibrahim Magun zai bawa hukumar EFCCn damar gudanar da ayyukanta ba tare da binciken da ake masa ya kawo mata rudani ba.

Fadar shugaban kasa ta cikin sanarwar ta ce wadanda ke ganin binciken da ake yiwa Ibrahim Magun a matsayin wata ‘yar manuniya ce ga rashin nasara a yakin da gwamnati mai ci ke yi da cin hanci da rashawa, shaci-fadi ne kawai suke yi domin kawo rudani a tsakanin ‘yan Najeriya.

A wani labarin kuma, kwamitin fadar shugaban kasa da ke binciken Ibrahim Magun ya kara bankado wasu zarge-zargen rashawa da ake yi wa dakataccen shugaban hukumar EFCCn.

Kamfanin dillancin labarai na NAN, ya ce rahoton da shugaban kwamitin mai shari’a Salami ya gabatar ya nuna yadda aka karkatar da naira biliyan 550 da hukumar EFCC ta kwato.

Jaridar NAN ta ce rahoton kwamitin kan abinda ake zargin an aiwatar a ranar 29 ga Mayu, 2015, zuwa 22 ga Nuwamba, 2018, ana ganin hakan wata alamar tambaya ce kan yadda ake karkatar da kudaden da hukumar EFCCn ke kwatowa daga hannun barayin gwamnati, karkashin ikon Ibrahim Magu.

Rahoton ya cigaba da cewa bincike ya nuna yadda rahoton sashen bibiyar al’amuran kudi ya bankado yadda EFCC ke aiwatar da wasu ayyukan badakalar kudade a tsakanin wasu manyan jami’an hukumar ciki har da Ibrahim Magun.

Binciken kwa-kwaf da NFIU ya gudanar ya bayar da rahoto kan yadda dakataccen shugaban hukumar EFCCn ke amfani da wasu hanyoyi ya na karkatar da kudade daga hukumar, a wasu lokutan ma yakan karbi na goro daga hannun wasu daga cikin mutanen da hukumar ke tuhuma da aikata almundahana.

A cewar rahoton sashen bibiyar yadda ake mu’amala da kudade a bankuna, akwai wani ofishin canjin kudade da ke da alaka da Magun wanda ke Kaduna, kuma yana dauke da asusun ajiyar banki sama da 158 inda ake ajiyar makudan kudade.

Haka zalika rahoton ya ce akwai wani lauya da yake da kusanci ko kuma alaka mai karfi da dakataccen shugaban EFCCn wanda ake biya ko kuma aka bashi naira miliyan 28.

Rahotanni sun ce ana tsammanin kwamitin binciken karkashin mai shari’a Salami zai cigaba da zaman tuhumar da ake yiwa Magun a ranar Litinin mai zuwa, yayinda lauyan Magun, Oluwatosin Ojaomo a ranar juma’ar da ta gabata ya nemi a bayar da belinsa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!