Labarai
Shugaba Buhari yana wasa da hankalin talakawa- Shamsuddin Kura
Wani matashin dan siyasa a jihar Kano mai hamayya da gwamnatin APC mai mulki Shamsuddin Kura da ake yiwa lakabi da wakilin talakawa ya bayyana cewa, bayyana zaben bara da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a matsayin sahihi abu ne da za a iya cewa kawai shugaban kasar yana yin wasa da tunanin ‘yan Najeriya ne.
Shamsuddin kura wakilin talakawa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Freedom Radio ta cikin sirin kowanne gauta wanda ta cikinsa ‘yan siyasa ke bayyana ra’ayoyinsu.
Ya ce idan aka yi la’akari da yadda shugaban kasar ya yi alkawarin ganin an gudanar da ingantaccen zabe da kuma kalamansa lokacin da ya je mahaifarsa watau garin Daura inda manema labarai suka tambaye shi ko idan ya fadi zabe zai taya wanda ya samu nasara murna? Inda shi kuma ya ce ai babu wanda zai lashe zaben sai shi, to a iya cewa tun a lokacin ya rushe maganar tasa da ya fada ta yin gaskiya a zaben.
Haka kuma ya kara da cewa kalaman na shugaba Buhari, kalamai ne da ko shi kansa ya zauna ya yi tunani zai san ya aikata ba dai-dai ba.
Haka kuma ya nuna takaicinsa bisa yadda shugaban kasa bai dauki mataki ba kan yadda aka samu rikici a zaben jihar Kogi da har ya yi sanadiyyar mutuwar wata shugabar mata ta jam’iyyar PDP, amma shugaban kasar bai ce komai ba kan lamarin, sabanin yadda irin haka ta taba aukuwa a jihar Lagos amma aka tura wakilai suka je domin jajantawa.