Labarai
Wasu cikin jami’an gwamnati a fadar Villa na yi wa Tinubu zagon kasa- El-rufai
Gwaman jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, ya ce, akwai wasu jami’ai a fadar gwamnatin tarayya ta Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja da sike yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, zagon kasa domin ya fadi a zabe.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne ta cikin wani shirin safe na gidan Talabijin na Channels.
Ya ce, wadannan mutanen da bai bayyana sunayensu ba suna cike da takaicin yadda Tinubu ya doke ‘yan takararsu a zaben fidda gwani, son haka suka shiga shirya makarkashiya domin ya fadi zaben.
El-Rufai ya kuma ce, mutanen na fakewa ne da muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin abin da yake ganin ya dace.
You must be logged in to post a comment Login