Coronavirus
Za’a bude makarantu a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a bude makarantu a kasar, bayan da suka dogon hutu saboda annobar Coronavirus.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da shugaban ya yi da kwamitin fadar shugaban kasa da ke sanya ido kan cutar Covid-19.
Sai dai ajujuwan da aka amince a bude a makarantu sun kunshi aji shida kadai a makarantun firamare, sai kuma aji uku da aji shida a makarantun sakandire, domin basu damar rubuta jarabawar karshe na kammalawa.
You must be logged in to post a comment Login