Labarai
Zamu sayar da mai kan N168 a Kano – IPMAN
Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa shiyyar Kano ta ce, zata sayar da litar man a kan N168.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Bashir Ahmad Ɗan Malam ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.
Ɗan Malam ya ce, hakan ya biyo bayan ƙarin da kamfanin mai na ƙasa NNPC ya yi.
A cewar sa, a yanzu za su riƙa sayo man a kan N155.75 maimakon 147,67 da su ke saye a baya.
Karin Labarai:
Majalisar wakilai taki amincewa da karin firashin man fetur
Karin farashin wuta da man fetur ya nuna Najeriya na cikin halin ni’yasu – Masani
Yaushe ƙarin zai fara?
Bashir Ɗan Malam ya ce, ƙarin zai fara ko wane lokaci daga yanzu, matukar gidan man ya siyo sabuwar oda.
Meye dalilin yin ƙarin?
Ɗan Malam ya ce, ba komai ya haifar da ƙarin ba sai janye tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi.
Ku kasance da mu a labaran mu na rana da ƙarfe 12 na rana domin jin cikakken bayanin da yayi da ma martanin wasu al’ummar ƙasar nan a kai.
You must be logged in to post a comment Login