Labarai
An dakatar da manyan ma’aikata 12 na hukumar EFCC
Manyan ma’aikata 12 ne na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC suka karbi takardar dakatarwa a jiya Litinin
Da yawa daga cikin na rike da manyan bincike na yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a halin yanzu.
Daya daga cikin ma’aikata da ya nemi a saka sunan sa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja cewa tun da suka fara aiki ba’a taba tuhumar su da laifi ba, amma sun rungumi kaddara kan wannan batun.
Tun farkon nadin Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC wasu na ganin cewa bai can-canci rike mukamin ba, la’akari da rahoton rashin can-canta game dashi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayar tun a wancan lokacin.
Rubutu masu alaka :
Za a janye ‘yan sandan dake aiki a EFCC
Hukumar EFCC ta gano ma’aikatan bogi 1000 a jihar Kwara
EFCC: ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji bada gudunmawar karya
Haka ma dai aka yi ta dambarwa a majalisar dattijai bayan da aka mika sunan Ibrahim Magu, inda ‘yan majalisu suka ki amincewa dashi, sai dai fadar shugaban kasa ta tsaya kai da fata akan ganin an tabbatar dashi a mukamin, wanda a yanzu kuma ake ganin sun raba hannun riga.
You must be logged in to post a comment Login