Labarai
COVID-19: Ma’aikata za su koma aiki a Katsina
Bayan daukar tsawon makonni ana zaman lockdown a jihar ta Katsina tun bayan da aka samu bullar cutar Covid-19, yanzu haka dai gwamnatin jihar ta umarci dukkanin ma’aikatan jihar kama daga matakin kananan hukumomi zuwa jiha, da su koma bakin aiki.
A wata sanarwa da gwamna Aminu Bello Masari ya fitar, gwamnatin ta kuma bude dukkanin kasuwannin jihar, bayan da aka samu raguwar masu dauke da cutar ta Covid-19 a fadin jihar.
Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Mamman Mai-Wake yace sun ji dadin wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka, la’akari da yadda suka fuskanci wani yanayi na matsi sakamakon zaman gida dole a jihar.
“Munji dadin wannan al’amari sosai, musamman mutanen da suke takure a gida sakamakon rashin harkokin kasuwanci” in ji shi.
Rahotanni sun ce da dama daga cikin ‘yan kasuwar da suka dogara da iya kasuwanci sun shiga halin ni ‘ya su sakamakon rashin samun kudaden shiga, yaynayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cak.
Lokacin da cutar Coronavirus ta yi ‘kamari a jihar Katsina ne gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe manyan kasuwannin jihar irin su Mashi, Dandume, Bakori da Jibiya da Mai-Aduwa, Jibiya, Kafur da Kankara da sauran kasuwannin da ke ci a kowanne mako.
You must be logged in to post a comment Login