Labaran Kano
Sauya wa tashar Sabon gari waje ne zai magance satar yara
Ma’aikatar mata da walwala ta Jihar kano ta ce, zata yi hadin gwiwa da hukumar Hisbah wajen magance matsalolin ayyukan badala da ke faruwa a tashoshin ababan hawa na Sabon Gari a cikin kwaryaar Kano.
Jaridar kanoFocus ta rawaito cewar ma’aikatun guda biyu na yawan samun kiraye-kiraye daga bangaren al’umma na bukatar cewar tashar ta tashi daga inda take zuwa wani wuri, sakamakon yawan sace yara tare da sauya musu adini da ake yi.
Yara goma da aka sace su dai wadanda suke zaune a wannan yanki ne ake zargin suka aikata wannan laifi.
A wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis, Dr Zahrau Muhammad Umar ta ce ma’aikatar ta zata yi hadin gwiwa da hukumar Hisbah ne don tabbatar da tsaftacewa tare da samar da tsaro a yankunann musammam a tashar ababen hawa da ke Sabon Garin.
Sanarwar dai mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a na ma’aikatar Hadiza Mustapha Namadi ta ce, kwamishinar Dr Zahrau ta bayyana haka ne a yayin da take karbar bakunci kwamandan hukumar ta Hisbah ustaz Harun Muhammad Ibn Sina a ofishinta.
Kwamishinar ta kara da cewa sakamakon yawan korafe-korafe da ake samu daga bangaren al’umma na irin ayyukan badala da ake aikatawa a tashar ne ya ja hankalin hukumarta bukatar sauran hukumomi don magance matsalar .
Sabon gari dai na makwabtaka da kabilu da dama wanda mafi yawansu ‘yan kabilar Igbo ne da sauran kabilu da ba Hausawa ba.
Tashar Sabon gari da tashar motoci ta Na’ibawa na daga cikin tashoshin da ake zargin ana safarar yara zuwa wasu birane a fadin Najeriya, musammam ma jihohin kudancin kasar.
Wasu daga cikin mazauna birni Kano dai sun nuna damuwarsu da cewar a wadannan tashoshi ne ake safarar miyagun kwayoyi zuwa jihohi daban-daban.
Wani lauya barista Umar Usman Dan Baito ne ya bukaci gwamna Ganduje da ya duba yiwuwar sauyawa tashar ta Sabon gari mazauni, ga yankin da ke da asalin yan gari kamar Dawanau wanda dama akwai babbar kasuwa a yankin.